Ƙirƙirar Sabbin Masarautu Zai Jawo Maka Mummunan Ƙarshe- Sheikh Ɗahiru Bauchi Ya Gargaɗi Ganduje

725

Sheikh Dahiru Bauchi, shahararren malamin addinin Musluncin nan kuma muƙaddamin ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, ya gargaɗi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da ya dakatar da shirinsa na dawo da sabbin masarautunsa huɗu, waɗanda Babbar Kotun Kano ta rushe.

Labarai24 ta ruwaito cewa Gwamna Ganduje ya aika da wani sabon ƙudiri zuwa ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda yake neman ƙara ƙirƙirar sabbin masarautu huɗu da ake ta cece-ku-ce a kansu a Rano, Gaya, Bichi da Ƙaraye, bayan kotu ta rushe su.

A ranar 21 ga Nuwamba, 2019, Mai Shari’a Usman Na’abba ya yanke hukuncin cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano ba ta bi ƙa’ida ba wajen zartar da dokar da ta kafa sabbin masarautun.

Amma, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Malam Garba Muhammad, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, ya ce ƙirƙirar sabbin masarautun “ya biyo bayan buƙatar da ake da ita na kawo masarautun gargajiya kusa da jama’a don sauƙaƙa gaggauto da ci gaban tattalin arziƙi da na tsaro a jihar”.

Mista Garba ya ƙara da cewa: “Wasu daga cikin waɗannan masarautun sun ma girmi Kano tun a tarihi, sai dai ƙoƙarin farfaɗo da su a Jamhuriya ta Biyu ya gaza cimma nasara.

Mutane da dama sun yi amanna cewa ƙirƙirar sabbin masarautun wata kutungwila ce daga Gwamna Ganduje don rage tasirin Sarki Muhammad Sanusi II bisa bambancin ra’ayin siyasa da yake tsakaninsu.

A wani saƙon murya da ya bazu a Intanet, kuma Labarai24 ta tabbatar da sahihancinsa, Sheikh Bauchi ya bayyana rashin jin daɗi da matakin Gwamna Ganduje na sake gabatar da ƙudiri don dawo da masarautun da kotu ta soke.

Ya shawarci gwamnan da ya yi watsi da duk wani shiri na ƙirƙirar sabbin masarautu a jihar don samun zaman lafiya.

“A matsayina ma muƙaddamin Tijjaniyya, na samu labarin da ba shi da daɗi cewa Gwamna Ganduje har yanzu yana son dawo da sarautu waɗanda hukuma ta ture, wato ɓangaren shar’ia ta ture, ya ce yana so wakilai su sake ba shi dama ya naɗa sarautun nan da kotu ta ture. Ina roƙon Ganduje don Allah don Annabi ya nema maza zaman lafiya a Najeriya ba Kano kaɗai ba domin dukkan mu ‘yan Tijjaniyyar Najeriya muna tare da Maimartaba Sarkin Kano, muna tare da Fadar Kano.

“Abinda ya taɓa wurin nan duka ya taɓa mu gaba ɗaya, kuma ba za mu ƙyale ba. Ina jawo hankalinsa da ya janye maganar nan, yadda kotu ta rushe waɗannan abubuwa nasa, to ya haƙura, ya mayar da Kano kamar yadda take kamar shekara 1000 da wani abu. Ya haƙura, abinda ya fi kyau, ya zauna lafiya da mutane, ya daina jawo wa kansa mummunar addu’a, ya daina jawo wa kansa gaba da jama’a”, in ji Shehi.

Ya ci gaba da cewa: “Mu ‘yan Tijjaniyya muna da yawa a Najeriya, ba Najeriya kaɗai ba duk inda muke ma muna tare da Fadar Kano, domin Fadar Kano ita ta kawo mana Shehu Ibrahim a Najeriya da kuma Afirka ma gaba ɗaya. Ba za mu mance da alherin da suka yi mana ba, saboda haka, muna tare da su, ba ma tare da duk wanda yake gaba da su. Saboda haka, muna jawo hankalin Gwaman Ganduje, ya bar maganar, yadda kotu ta rushe ta mayar da Kano kamar yadda take a da, ya bar ta ita ma ta zauna kamar yadda take. Ina jawo hankalinsa kar ya jawo mana fitina da tashin hankali da rashin zaman lafiya.

“Mu fa dukkan ‘yan Tijjaniyya gaba ɗaya, da mu da masoyanmu muna tare da Sarkin Kano muna tare da Fadar Kano. Duk abinda ya taɓa wurin nan ya taɓa mu ba za mu ƙyale ba. Mu ko ba mu da ƙarfi muna da addu’o’i. Saboda haka muna jawo hankalin Ganduje da ya janye wannan maganar, ya bar Kano kamar yadda take kamar yadda ya same ta, kamar yadda iyayensa suka samu Kano, ya bar ta haka”.

“Nasara ya zo ya yi shegantakarsa shekara 60 bai taɓa birnin Kano ya yi mata kaca-kaca kamar yadda Ganduje ya yi ɗinnan wannan ba. Mulkin soja ya zo ya bar Kano lafiya lau kamar yadda aka same ta. Amman ya kamata shi ma ya yi wa kansa wa’azi ya raba kansa da fitina da tashin hankali, ya bar Kanon yadda Allah Ya yi ta. Tunda take shekara da shekaru, a maganar cewa za a sake yin sarautu a Kano a faffasa Kano, a wargaza Kano, wannan mummunar shawara ne”, in ji Shehin malamin.

“Ina jawo hankalinsa ya yi wa kansa ƙiyamullali, ya rufa wa kansa asiri, kar ya jawo wa kansa tsinuwa da yawa wa bakin ‘yan Tijjaniyya da addu’o’i munana a wajen ‘yan Tijjaniyya. Mu muna tare da Sarkin Kano da Fadar Kano, mu ‘yan Tijjaniyya duk inda muke, duk abinda ya taɓa wurin nan ya taɓa mu, ba za mu ƙyale ba kuma.

“Kano, tun zamanin Fodiyawa suna cewa ƙasan Fodiyawa gaba ɗaya, garin da ya fi kowane gari albarka in ji Shehu Ɗan Fodiyo da ‘ya’yansa, su Muhammad Bello da ƙannensa su Abdullahi, gari mafi albarka, Kano”, a kalaman Shehi.

“Shehu kuma, Shehu Ibrahim, Radiyallahu anhu ya zo, ya ce Kano Allah Ya yi mata albarka kullum da kullum, yana ce ni na fita daga Kano amma zuciyata tana Kano, don me? Saboda masoyana suna Kano. Yana nufin duk jama’ar da yake saduwa da su a Kano su ne masoyansa na Kano. Saboda haka, ina jawo hankali ina maimaita wa Ganduje nasiha, ya ajiye fitinar nan na karkasa Kano da farfasa Kano, ya bar Kano kamar yadda ya same ta, kamar yadda iyayensa suka same ta, ya fi masa zaman lafiya, ya ƙare aikinsa na gwamnati yana cikin zaman lafiya ya fi masa ya ƙare ana turka-turka da shi ana tsine masa ana zargin sa, ba kyau.

“Mutum yana nema wa kansa kyakkyawar makoma da kyakkyawan ƙarshe, ba ya nema wa kansa mummunar makoma da mummunan ƙarshe. Taɓa Fadar Kano ɗin nan taɓa mu ne gaba ɗaya mu ‘yan Tijjaniyya da masoyanmu duk inda muke, ba Najeriya kaɗai ba duk inda muke. Ina fatan Gwamna Ganduje ya ji wannan shawara da na ba shi. Allah Ya sa ya yi aiki da ita, ya bar Kano ta zauna lafiya kamar yadda ya same ta.

“Muna fata masu hankali daga cikin mutane na Kano su matsa kusa da shi su yi masa wa’azi, su gaya masa gargaɗi cewa abinda ya sa a gaba ɗin nan ba ya da kyau, ba zai yi masa kyau ba. Zai kawo masa abinda ba shi da kyau, Allah Ya kiyaye”, Shehi ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

2 Sako

  1. Assalam Amma governor Ina maibaka shawara kanutsu dakyau da bakada farinjini dayawa ga kanawa Amma hakuri akan kudurinka na nada sabbin masarautu zai jama farinjini maiyawa Mai girma governor yanadakyau kasani mulki kakeyi ba ayima Al umma dole munce bamayi bamaso kayi hakurimana munafatan samun shugabancin kasa nangaba saboda kana aiki yadda yadda Amma Taya haka zatayiwu mubaka ku r unmu baka yimana abinda mukeso natabbata duk abunda zakanema nangaba in harkarasa kano kamar karasa muradinkano mulki akwai Dadi bazakasan hakaba sai kasauka Amma katambayi kwankwaso kaji ya yakeji yanzu inda Ana sayarwa daya sayanzune yafi sonmulkin daya kubucemasa haba gangaram inkaki jinmagana muka alarammomi Mai zakacemana.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan