Buhari Ya Nada Dan Wasan Kwaikwayo Nura Hussain Kwamishina

691

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattawan kasar nan sunn shugaba tare da kwamishinonin da kuma Membobin da wakilan hukumar alhazai ta kasa wato NAHCON.


Daga cikin sunayen wadanda shugaban kasar ya aike zuwa majalisa har da sunan fitaccen jarumin nan na shirin fina-finan Hausa wato shahararren Nura Hussaini Yakasai, wanda aka bashi Kwamishin Tsare-tsare da Kudi na hukumar, daga shiyyar arewa maso yamma.
Sauran jerin sunayen sun hada da:


1. Zikrullah Olakunle Hassan ~ Shugaba(Daga jihar Osun)2. Abdullahi Magaji Hardawa~ Kwamishina Sintiri (Bauchi)
3. Nura Hussaini Yakasai~ Kwamishinan Kudi da tsare tsare (Kano)
4. Sheikh Momoh Suleiman~ Kwamishinan Yada Labarai da Kididdiga (Edo).

Ana kallon dai ana tukuici da fadar shugaban kasa ta fara yiwa yan wasan kwaikwayon, la’akari da yadda su ka bayar da gudummawa ga jam’iyyarr APC da kuma shugaba Muhammadu Buhari a lokacin zaben shekarar 2015

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan