Kan ‘Yan Majalisar Dokokin Kano Ya Rarraba Bisa Sabuwar Dokar Masarautu

361

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano sun gaza cimma matsaya bisa Sabuwar Dokar Masarautu ta 2019 wadda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aika musu don dawo da masarautu huɗu masu daraja ta ɗaya da Babbar Kotun Kano ta rushe.

Majiyarmu ta ruwaito cewa a ranar Laraba ‘yan Majalisar Dokokin suka shafe kimanin sa’o’i uku a asirce a zauren Majalisar suna muhawara a kan ƙudirin dokar ba tare da cimma matsaya ba.

Idan dai za a iya tunawa, gwamnatin jihar Kano ta amince da wata sabuwar doka wadda za ta dawo da masarautu huɗu a Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya waɗanda kotu ta rushe.

A ranar 21 ga Nuwamba ne kotun, wadda Mai Shari’a Usman Na’abba ya jagoranta ta yanke hukuncin cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano ba ta bi ƙa’ida ba wajen zartar da ƙudirin dokar da ta ƙirƙiri sabbin masarautun.

Majiyoyi sun faɗa wa majiyarmu cewa wasu daga cikin ‘yan Majalisar ba sa farin ciki da yadda ake tafiyar da batun sabuwar dokar.

An gano cewa da yawa daga cikin ‘yan Majalisar suna so a bi tabbatattun ƙa’idojin Majalisar wajen zartar da dokar, wanda ya haɗa da ji daga jama’a, ba kamar yadda aka zartar da dokar da ta gabata ba a gaggauce.

Majiyoyin sun bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan Majalisar sun bayyana damuwa bisa “ɗimbin iko” da aka ba Gwamna Ganduje a dokar, ikon da ya haɗa ikon naɗa masu naɗa sarki, da kuma yi wa masarautun kasafin kuɗi.

Wani batu kuma da ya raba kan ‘yan Majalisar shi ne wani sashi a dokar wanda yake neman hana sarakuna bada shawara ga gwamna har sai gwamnan ya buƙata.

An gano cewa wannan batu, an fassara shi a matsayin wani yunƙuri na hana sarakunan ‘yancin faɗar albarkacin baki, wani abu da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bada dama.

Majalisar ta ɗage zamanta zuwa gobe Alhamis don ci gaba da muhawara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan