Kano Pillars Sun Sami Nasarar Farko Awaje

217

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tasami nasarar farko awaje acigaba da buga gasar ajin Premier ta kasar nan.

Sun sami nasarar ne ahannun kungiyar kwallon kafa ta Akwa Starlets na jahar Akwa Ibom daci 2 da 1 ta hannun dan wasa Nwagua adaidai mintina na 27 da kuma 78.

Yaudai shine karon farko da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tafara jefa kwallo kuma yace ta sami nasarar farko.

Ita dai Akwa Starlet batayi rashin nasara ba tunda ta fara buga gasar a bana sai yau.

Yanzu dai Masu Gida wato Kano Pillars suna da maki 6 daga wasanni 6 da suka fafata harda kwantan wasan yau da suka lashe Akwa Starlet inda awasanni shidan da suka buga suka yi kunnen doki 3 suka lashe wasa 1 aka lashesu awasa 2.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan