Home / Labarai / Dai-daituwar Al’amura A Laberiya Na Daga Manyan Abubuwan Da Na Sa A Gaba- Buhari

Dai-daituwar Al’amura A Laberiya Na Daga Manyan Abubuwan Da Na Sa A Gaba- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce dai-daituwar al’amura a Laberiya yana daga manyan-manyan abubuwan da ya sa a gaba da suka shafi zaman lafiya, daidaituwar al’amura da arziƙi a Nahiyar Afirka ta Yamma.

Shugaban Ƙasar ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Mawine Diggs, Wakiliya ta Musamman ta Shugaban Laberiya, George Weah, kuma Muƙaddashin Ministar Ƙasashen Waje a Fadar Gwamnati dake Abuja, ranar Laraba.

Wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Shugaba Buhari Kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu ya fitar ta jiyo Shugaba Buhari yana cewa: “Zan ci gaba da yin dukkan mai yiwuwa don tabbatar da dai-daituwar al’amura a Laberiya”.

Ya yaba wa Shugaban na Laberiya bisa ƙoƙarin da yake yi na kyautata dangantaka da Najeriya.

Wakiliyar ta musamman ta ce ta kawo gaisuwa ta musamman daga Shugaba Weah da al’ummar Laberiya, ta kuma gode wa Shugaba Buhari bisa “ɗimbin goyon baya” da yake ba ƙasarta.

Miss Diggs ta ce goyon baya da tallafin da Najeriya “sun yi kyakkyawan tasiri” ga Laberiya da al’ummarta.

Ta ƙara da cewa ta kawo saƙo na musamman daga Shugaba Weah biyo bayan tattaunawa da aka yi kwanan nan tsakanin shugabannin kasashen biyu.

Shugaba Buhari ya yi alƙawarin bada amsa da ta dace kuma cikin gaggawa ga rubutaccen saƙon da ta kawo.

About Hassan Hamza

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *