Home / Labarai / Majalisar Dokin Jihar Kano Ta Amince Da Dokar Ƙarin Masarautu 4 A Jihar Kano

Majalisar Dokin Jihar Kano Ta Amince Da Dokar Ƙarin Masarautu 4 A Jihar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da sabon kudirin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika mata na kafa sababbin masarautu guda hudu na Bichi, da Rano da Gaya da kuma Ƙaraye.


Tun da farko gwamna Ganduje ya bi umarnin Kotun da ta yanke hukunci cewa dokar da aka yi ta farko ba’ayi ta bisa ka’ida ba, in da gwamnan ya kakkaɓe dokar yai mata garanbawul sannan ya sa ke turawa Majalisa.

Bayan tsallake karatu na farko da na biyu da kuma na uku a ƙarshe majalisar ta zartar da ita, ana sa ran majalisar za ta mayarwa da gwamna Ganduje domin ya sa hannu nan bada jimawa ba.

Idan za’a iya tunawa makwanni biyu da wata babbar kotun jihar Kano ƙarƙashin mai shari’a Usman Na’abba ta soke naɗin sabbin sarakunan da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi, in da ta ayyana matakin a matsayin wanda ya saɓawa doka, yayin da ta bukaci a koma kan tsarin da ake kai kafin ta kammala sauraren ƙarar da aka shigar a gabanta.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *