NNPC, FIRS Da DPR Sun Yi Almundahanar Triliyan N1.5- Babban Mai Binciken Kuɗi

195

Daga cikin triliyan N6.4 da hukumomin tattara kuɗaɗen shiga suka tara a 2017, an wawure kimanin triliyan N1.5 kuma ba a dawo da su zuwa Asusun Gwamnatin Tarayya ba, abinda ƙarara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗin na Ƙasa ya bayyana haka a cikin rahotonsa na binciken kuɗi na 2017 wanda ya saki a Abuja ranar Laraba.

Rahoton, wanda Babban Mai Binciken Kuɗi na Ƙasa, Anthony Ayine ya sanya wa hannu, ya ce hukumomin huɗu sun fitar da kuɗaɗen ne ba tare da samun izini ba.

Hukumomin da suka yi almundahanar kuɗaɗen su ne Kamfanin Albarkatun Man Fetur na Ƙasa, NNPC, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa, FIRS da Sashin Albarkatun Man Fetur, DPR.

Rahoton mai shafi 320 ya ce yayinda NNPC ya tara jimillar kuɗi naira triliyan N2.41, ya kwashe triliyan N1.3 kafin ya mayar da canjin triliyan N1.07 zuwa ga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Rahoton ya ce DPR kuma ya tara biliyan N733.05, ya kwashe tare da biyan biliyan N26.77 zuwa wani asusu mai suna ‘royalty account’, kafin ya mayar da canjin biliyan N706 zuwa ga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Haka kuma, rahoton ya ce FIRS ta tara triliyan N2.66, amma ta mayar da triliyan N2.45 zuwa ga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Mista Ayine ya bayyana damuwa bisa yadda ake kwashe kuɗaɗe, yana mai cewa hakan ya yi mummunan tasiri a kan kuɗaɗen da ake rabawa tsakanin gwamnatoci uku.

Ya bada shawara ga Babban Akanta Janar na Ƙasa, Ahmed Idris, cewa dole a dakatar da duk wasu kuɗaɗe da ake cirewa daga tushe saboda sun saɓa da Sashi na 162 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Ya ƙara da cewa duba da waɗannan kwashe-kwashen kuɗaɗe, za a hukunta dukkan hukumomin da suke da laifi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan