Ra’ayin Sheik Umar Kwangila
Ba wai ana maganar jam’iyya ba ne a yayin da ake zawarcin mafitar Arewa da Nijeriya baki daya.
Idan ana neman mai kishin al’umma ba a neman mai kishin jam’iyya. Idan ana neman mai gina gari da al’umma ba a saurarar mai rushe-rushe. Tabbas, ba Kanawa kawai ke da wannan darajar ba tunda Kwankwaso ruwan dare ne game duniya.
Da wannan nake kira ga al’ummar Nijeriya da su cigaba da nuna goyon bayan su ga Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso dan takarar kujerar shugabancin kasar nan a shekara ta 2023 Insha Allah.
Ba a yi mutum mai kishin cigaban al’umma a wannan lokaci irin Madugu ba. Wallahi ba ina wannan maganar a kungiyance ba ne, saboda ni ba dan Kwankwasiyya ba ne.


Turawa Abokai