Ba Ma Goyon Bayan Taɓa Masarautar Kano -Majalisar Shura Ta Tijjaniyya

389

Majlissar shura ta ɗariƙar Tijjaniyya reshen jihar Kano ta bakin Khalifa Sani Shehu mai Hula ta bayyana Matsayinta akan abin da ya ke faruwa tsakanin gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano.

Khalifan yace majalissar ta shura da ta ƙunshi ɗumbin mabiya ɗariƙar Tijjaniyya na Lura da abin da ya ke faruwa tsakanin gwamnati da masarautar Kano, wanda hakan ya na damun dukkanin wani ɗan ɗariƙar Tajinniyya.

Ya ƙara da cewa “a baya wannan majalisa ta sadu da Mai girma gwamnan Kano da mai martaba Sarkin Kano kuma kowannensu an same shi har sau biyu domin warware waɗannan al’amura, kuma ta ba da shawarwari wanda a hangen ta in an bi su za su warware duk waɗannan matsaloli, amma a ƙarshe a yanzu ya fito fili cewa waɗannan shawarwari ba’a sauraresu ba”

Khalifa Sani Shehu Mai Hula ya ce yanzu majalisar Shura ya zamar mata dole ta fito fili ta bayyana matsayinta wanda shi ne duk ƴan Tijjaniyya na goyen bayan abin da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya faɗa a kafafen yaɗa Labarai.

“A bisa wannan mu ke bayyana cewa taɓa Masarautar Kano abu ne wanda ba za mu taɓa goyon baya ba” In Ji Khalifa Sani Shehu Mai Hula

Madoga Aminic Radio, Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan