Hukumar DSS Ta Saki Omoyele Sowore Bayan Ya Shafe Sama Da Watanni 3 A Tsare

171

An kama Sowore ne a ranar 2 ga Agustan 2019 bayan ya kira wata zanga-zangar gama-gari ƙasar nan.


Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sa ki Omoyele Sowore bayan ya yi fiye da wata uku a hannunta, kamar yadda lauyansa Femi Falana ya tabbatar wa da BBC.

Tun da farko dai babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bai wa hukumar tsaro ta DSS umarnin yin hakan a ranar Alhamis, inda ta ce a sake shi cikin sa’a 24 tare da biyansa diyyar naira ₦100,000.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta ce umarnin ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.

Har ila yau ta ce ba zai yiwu hukumar DSS ta mayar da kanta kamar kotu ba, sannan kuma ta bayar da umarnin sakin abokin shari’ar Sowore mai suna Olawale Bakare.

Hukumar DSS ta ce ta tsare Sowore ne saboda zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon kiran juyin juya hali da ya yi – ya yi masa lakabi da #RevolutionNow.

Omoyele Sowore shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a intanet.

Daga cikin laifukan da ake zarginsa da su har da tsokanar Shugaba Buhari a shafukan sada zumunta.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan