Ɗaya Daga Cikin Ma’aikatan Labarai24 Ya Angwance

300

Yau asabar 7 ga watan Disamba Abubakar Muhammad Usman ya angwance da amaryarsa Rabi’a Ahmad Shuaib.


Abubakar na ɗaya daga cikin haziƙan ma’aikatan jaridar Labarai24, wanda mu ke alfahari da shi akan irin ƙwazonsa.


Tun da farko dai an ɗaura auren ne a masallacin juma’a na tsohuwar jami’ar Bayero da ke Kano, in da ya samu halartar ɗimbin al’umma daga ciki da wajen jihar nan.


Muna adduar Allah ya sanya alkhairi a wannan aure tare fatan samun zuri’a ɗayyiba. Waɗanda su ka samu halarta kuma muna yi musu bangajiya tare godiya mai yawa

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan