Ban Taɓa Karɓar Albashina Ba, Haka Ma Fansho – Bafarawa

227

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa bai taba karbar fansho a matsayinsa na tsohon gwamna ba.

Ya bayyana haka ne a tattaunawa da BBC ta yi da shi a cikin shirin Ra’ayi Riga a ranar Juma’a, inda ya shaida cewa ko da yake rike da mukamin gwamna bai taba karbar albashi ba, hasali ma tuni ya “bayar da albashinsa ga Hubbaren Shehu Usman Danfodiyo.”

Bafarawa ya ce ya yi mamaki da ya ji an ce wasu tsofaffin gwamnoni na karbar miliyan 10 a duk wata.

Ya kuma ce duk wasu hakkoki da ake ba tsofaffin gwamnoni kamar su gidaje da motoci da kula da lafiya “bai taba samu ba.”

Maganar fansho na gwamnoni ta tayar da kura a ‘yan kwanakin nan tun bayan da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya nemi gwamnan jihar mai ci, Bello Matawalle da ya biya shi dukkan hakkokinsa da doka ta tanada da suka hada da fanshon naira miliyan 10.

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa fiye da jihohin Najeriya 20 ne suke da dokar fansho ga tsoffin gwamnoni da mataimakansu da shugabannin majalisun jihohin.

Bayan fara wannan takaddama, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Balarabe Musa ya shaida wa BBC, yana karbar naira 700,000 a duk wata, a matsayin fansho.

Shi kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa naira 667,000 ya ke karba.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan