BUK Ta Ƙara Kuɗaɗen Ɗakunan Kwanan Ɗalibai, Sauran Caje-Caje

288

Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ta ƙara kuɗaɗen ɗakunan kwanan ɗalibai da sauran kuɗaɗen gudanarwa ga ɗalibai masu karatun digiri na farko da masu karatun gaba da digiri na farko.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Majalisar Dattijai ta jami’ar ta amince da wannan ƙarin kuɗaɗe ne a taron tattaunawarta karo na 387, kamar yadda mujallar BUK ta bada rahoto.

Magatakardar Jami’ar, Amina Umar Abdullahi ta bayyana cewa an ƙara kuɗaɗen ɗakunan kwanan ɗalibai ga ɗalibai ‘yan Najeriya masu karatun gaba da digiri na farko daga N12,150 zuwa N25,150.

Misis Abdullahi ta ce ɗalibai ‘yan ƙasashen waje masu karatun gaba da digiri na farko za su biya N80,000 a shekarar karatu ta 2019/2020 mai kamawa, maimakon N60,000.

Haka kuma, ɗalibai masu karatun digiri na farko farko za su biya N20,090 a matsayin kuɗin kwanan ɗaki, maimakon N12,090 da suke biya a baya, yayinda gado ba tare da katifa ba a yanzu zai kama N12,090, maimakon N7,090 da ake biya a baya.

Bugu da ƙari, jami’ar ta ƙara kuɗin amincewa da karɓar gurbin karatu ga dukkan ɗalibai masu karatun digiri na farko daga N5,000 zuwa N10,000.

Misis Abdullahi ta ƙara da cewa a halin yanzu, duk wanda yake son ƙara karɓar sakamakon karatu na wucin gadi zai biya N1,000 ne, maimakon N500 da ake biya a da.

Magatakardar ta kuma sanar da shigo da sabbin caje-caje na kuɗaɗen gudanarwa.

A ta bakinta, a halin yanzu, duk mai son karɓar Takardar Shaidar Ƙwarewa ta Turanci, sake karɓar takardun samun gurbin karatu, ko gyara suna a kan takardar samun gurbin karatu zai biya N1,000 ga kowane.

Ta ƙara da cewa za a riƙa cazar N500 ga wanda yake son sake fitar da Fama-Famai na Rijistar Kwasa-Kwasai, CRFs, ko yake son sake fitar takardar shaidar biyan kuɗin rijista.

Majalisar Dattijan ta BUK ta kuma ɓullo da biyan ƙarin N3,000 ga ɗaliban ‘Pharmaceutical Science’ da kuma N20,000 ga ɗaliban ‘Architecture’.

Sauran caje-caje da Majalisar Dattijan ta amince su sun haɗa da N5,000 da ɗaliban B.Sc da B.Sc (Ed) Geography za su riƙa biya a Makarantar Faɗaɗa Ilimi, da kuma N10,000 da ɗaliban aji 500 na waɗannan ɗalibai biyu za su riƙa biya don yin tafiye-tafiye na ilimi.

Magatakardar ta ƙara da cewa Majalisar Dattijan ta BUK ta kuma ƙara kuɗaɗen shiga ƙungiyoyin ɗalibai daga N200 zuwa N300, kuɗaɗen da a halin yanzu za a riƙa biya a lokacin yin rijista daga shekarar karatu ta 2019/2020.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan