Home / Labarai / Gudaji Kazaure Ya Soki Kasafin Kuɗin Bana

Gudaji Kazaure Ya Soki Kasafin Kuɗin Bana

Cikin jawabai ko tsokaci da ya saba gudanar wa, wakilin ƙananan hukumomin Gwiwa da Kazaure da Roni da kuma Ƴan Kwashin jihar Jigawa a majalisar ƙasa Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana takaicin sa game kasafin kuɗin bana, bayan da majalisar ta amince da shi.


Gudaji kazaure yace abin takaici ne yadda kunshin kasafin kudin bana ya mayar da hankali kan manyan ayyuka, wanda a cewar sa ba shi ne bukatar talakawan ƙasar nan ba.


A cewar Gudaji ba hanya ce buƙatar ƴan najeriya wanda mafi yawansu talakawa ne ba, a basu aikin da zasu samu kudin shiga a duk karshen wata shi ne mafi soyuwa.


Wakilin yaja hankalin majalisar ta tuna abinda ya faru lokacin da ake rajistar daukar aiki a rundunar civil defence, inda sama da mutane miliyan uku suka yi rajista, a guraben da basu wuce dubu goma ba.


Gudaji kazaure yayi mamakin inda hankalin shugabanni akan lakabin da aka yiwa kasafin kudin, wato kasafin gyara kasa, wanda sunan sa ya sha ban ban da abinda ya kunsa.


Ya jaddadawa shugaban majalisar cewa daukar aiki a halin da ake ciki yafi ginin hanyoyin da ba zasu amfanawa rayuwar talaka komai ba.


“Muna ganin gwamnatoci na ginin hanyoyi da gadoji, shi mutane zasu ci su kwana?”
Yace irin wannan ce ke haifar da aikata manyan laifuka, tunda mafi yawan wadanda ake kamawa sun kammala karatun jami’a babu aikin yi.


A ganin sa ba dai dai bane rage yawan matasa da za’a dauka aikin jami’an tsaro na civil defence daga dubu goma zuwa dubu biyar.


Rahoton Dala FM Kano

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *