Gwamnatin Jihar Kano Ta Ɗauki Ma’aikatan Kiwon Lafiya Guda 920

184

A ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na cigaba da inganta sashen kula da kiwon lafiyar al’umma, gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa takardun shaidar ɗaukar aiki na dindindin ga sabbin ma’aikatan lafiya da gwamnatinsa ta ɗauka aiki kimanin mutum 920.

Taron miƙa takardun shaidar ɗaukar aikin ya gudana a ɗakin taro na Coronation Hall da ke cikin gidan gwamnatin Jihar Kano, in da gwamnan ya bayar da tabbacin haɗe cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko ƙarƙashin inuwa guda.

“Haɗe cibiyoyin kula da lafiya guri guda zai taimaka wajen ƙara inganta sha’anin kulawa da kiwon lafiya tare da ƙara kyautata aiki yadda ya kamata”. Inji gwamna Ganduje.

“Hikimar haɗe hukumomin kula da kiwon lafiya matakin farko ƙarƙashin inuwa ɗaya, za a samu sauƙin gudanarwa ta fuskar ma’aikata da kuma kuɗaɗen gudanarwa haɗi da samar da alaƙar aiki mai ƙarfi da kuma inganci a tsakanin ma’aikata”.

A nasa ɓangaren kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya yabawa gwamna Ganduje akan irin cigaban da ya samar a fannoni daban-daban na kiwon lafiya

Daga ƙarshe kuma Dakta Tsanyawa ya godewa dukkan sassan hukumomin samar da cigaba a fannin lafiya akan irin jajircewarsu da kuma gudunmawar da su ke bayarwa wajen cigaban tsarin kiwon lafiya a Jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan