Jaruma Rahama Sadau Ta Cika Shekaru 26 Da Haihuwa: Me Ka Sani Game Da Ita?

203

An Haifi Jarumar Kannywood Rahama Sadau A Garin Kaduna A Unguwar Sarki a ranar 7 ga watan Disambar Shekarar 1993

Ta Yi Karatun Gaba Da Sakandire A kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna in da ta Samu Shaidar Harkokin Kasuwanci Wato (Business Admin)

Ta samu damar halartar jami’ar mediterranean da ke arewacin ƙasar Cyprus, in da ta samu digiri akan Human Resource Management

Rahama Sadau Dai Jaruma Ce Wadda Ta Yi Fice A Fannin Wasan Kwaikwayo Na Masana’antar Kannywood Inda Ta Fara A Shekarar 2013.

A Wannan Zamani Ta Sahara A Harkan Shirin Fim Din Kannywood, Abu Ne Mawuyacin Ne A Samu Wani Ko Wata Da Basu San Jarumar Ba Musamman Saboda Yadda Ta Yi Fice Wajen Iya Tikar Rawa.

Jaruma Rahma Sadau Ta Kware Wajen Iya Yin Magana Da Yare Uku, Hausa,Turanci Da Kuma India

Jarumar Ta Fara Ne Bayan Da Ta Fito A Fim Din Gani Ga Wane Tare Da Ali Nuhu.

Bayan Wannan Fim Ne Kuma Sai Ta Cigaba Da Samun Shiga Manyan Finafinai.

Wannan Nasara Ce Kuma Ta Bata Damar Shiga Zuwa Masana’antar Shirya Fina-Finan Kudancin Najeria.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan