Aci gaba da buga gasa mai daraja ta biyu ta kasar nan wato Nigerian National League wasan mako na 3 kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes dake jahar Niger ta casa kungiyar kwallon kafa ta EFCC dake babban birnin tarayya Abuja.
Tornadoes dai ta casa ta daci 1 mai ban haushi ayammacin yau Asabar.

Yazuwa yanzu dai ba a sami nasara akan Niger Tornadoes ba tunda akafara wannan gasa.
Mai horas da kungiyar kwallon kafan ta Niger Tornadoes wato Abubakar Bala ya bayyana cewar ya gamsu da nasarar da kungiyar sa ta samu inda ya kara da cewa a duk karshen wasa abin da ake da bukata shine maki 3 kuma sun samu.
Turawa Abokai
[…] Muƙalar Da Ta GabataNiger Tornadoes Sun Lashe EFCC Awasan Mako na Uku […]