Za’a Yi Bikin Sauyawa Wani Matashi Suna Zuwa Buhari A Kano

847

Wata majalisar masoya gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ke da matsuguni a titin gidan zu a birnin Kano sun bayar da wata sanarwar bikin canjin sunan ɗaya daga mambobin wannan majalisa na ainihi zuwa sunan shugaban ƙasa MUHAMMADU BUHARI

Tun da farko dai majiyar Labarai24 ta ci karo da takardar gayyatar ne a shafin fitaccen ɗan jaridar nan na gidan rediyon Freedom Dutse wato Bilyaminu El-Idris Tudun Wada

Sanarwar ta bayyana cewa a gobe lahadi ake sa ran gabatar da shagalin bikin canjin wannan suna akan titin gidan namun daji da ke Kano wato Zu rod

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan