Yawaitar Mutuwar Aure A Ƙasar Hausa: Ina Gizo Ke Saƙar Ne? – Jiddah Gaya

380

Ko shakka babu aure wani halastaccen ginshiki ne na zamantakewa a tsakanin namiji da mace, domin kariya daga fasadi, ɓarna da kuma sharrin luwaɗi da sauran laifuka. Duka, a addinance da kuma al’adance, namaji ne ke zuwa ya nemi mace da aure ta hannun iyayensa daga iyayenta.

Hakika yawaitar mace-macen aure babban kalubale ne, kasancewa aure shine ginshikin samarwa da kuma gina kowace al’umma.Tabarbarewar wannan muhimmin al’amari (aure) matsalace babba da take kusan shafar al’umma baki daya.

Aure sha’ani ne da yake bukatar kulawa ta musamman duba da kasancewar sa jigo na rayuwar kowani mutum namiji ko mace.

Hakika mace-macen aure na bani tsoro matuka a wannan lokacin, anyi sakaci sosai da aure, inda a halin yanzu mace-macen auren ya kusa zama ruwan dare acikin al’umma.

Lokuta da yawa in ka bibiyi dalilan mutuwar aure zaka gane cewa tun da fari ba’a gina auren yadda ya dace ba, ma’ana ba’ayi shi bisa kyakkyawar manufa ba ko Kuma a samu wani bangaren ya boye manufar marsa kyau aransa wanda daga bisani in akayi auren ya gaza cimma wannan boyayyar manufar sai matalsaloli su fara danno kai.

Tabbas mutuwar aure babban kalubale ne wanda yana daya daga cikin abubuwan da suke haifar da matsaloli masu tarin yawa. Yayin da aka samu mutuwar aure, matsaloli da dama na shafar bangarorin da auren ya hada, kama daga su ma’auratan, yaran da suka haifa, Iyayen su wasu lokutan ma da jama’ar dake kusa dasu.

Yara su suka fi shiga matsala ko kuma cutuwa a lokacin da aka samu rabuwa tsakin maihaifansu wanda sanadiyar hakan mahaifiyar kan tafi ta barsu a lokacin dasu ke bukatar kulawarta da kasancewa a tare da ita. Sau tari akanyi rashin sa’a Uba ya auro wadda baza ta kula da dauwainiyar yaran da tarbiyyar su yadda ya kamata ba.

A takaice rayuwar yaran da iyayen su suka rabu na shiga wani hali ko su tagayyara koma su fada wata mummunar hanya. Dukka wadannan na faruwa ne sakamakon rashin hakuri, ko rashin tunbubar manya ko kuma gajen hakuri wajen lalubo mafita a lokacin da al’amuran auratayyar suka rintace.

To, masu iya magana na cewa kowa ya tuna bara to baiji dadin bana ba, tabbas wannan haka yake domin idan aka kwatanta yawaitar mace-macen aure da matsalolin auren a baya ko kama kafar na yanzu basuyi ba.

Haka kuma, mutanen da su ka yi aure shekara goma ko sha biyar baya karma mu Kai da nisa, baza ka kwantantasu da Mutanen yanzu ba ta fuskar: wayewa da sanin dabaru da hikimomi a zamanance.

Amma me? Auratayyar su tafi ta yanzu karko duk kuwa da takamar wayewa da muke da ita, to a iya cewa wayewar bata haifar da ‘Da mai ido ba, tun da a kullum matsalar yawaita take .

Na kanyi mamaki kwarai idan naga saurayi da budurwar da su ka yi soyayya kamar su hadiye juna auren su ya mutu a kasa da shekara. Baya da wannan, wani abu dana kara lura dashi shi ne matan yanzu musamman yan’mata in dai ta fuskar ado, kwalliya, wayewa, iyayi kala- kala, sannin girke-girke iri iri na zamani ba zaka hadasu dana baya ba amma duk da tarin wadannan auratayyar wannan lokacin ko kama kafar matan dake da karancin wadannan abubuwan batayi ma’ana matan bayan da ake wa kallon basu da wayewa.

To ina gizo ke sakar? Rashi girmama juna, rashin hakuri da rashin ganin mutuncin juna abubuwane da su ka yi karanci sosai a tsakanin ma’auratan wannan lokaci, wanda a baya sam abin ba haka yake ba dan ko Butar Alwala ta miji matan da na bata girma balle kuma mai Butar.

Saboda haka, akwai bukatar komawa baya domin ko yi da kyawawan dabi’u na auratayyar mutan da wanda suka hada da: Ladabi, biyayya, kunya, kawaici, hakuri, iya magana, daraja iyayen kowani bangaren na ma’auratan, da sauran su domin kawo karshen ko Kuma dakile matsalar yawaitar mace-macen aure akan dalilan da basu taka kara sun karya ba.

Sannan, akwai bukatar gina shi auren akan manufa mai Kyau da Kuma tsoron Allah, domin kusan za’a iya cewa, yanzu an sauka daga kan tsari ba’a kyautata niyya a sha’anin aure wanda sakamakon haka sai matsaloli su ta aukuwa.

Shigar da manya yayin da wata Matsala ta faru domin samun kyakkyawar mafuta.

Yawaitar mutuwar aure a tsakankanin ƙabilar Hausawa hakan ya sanya Hausawa su ka zama ƙabila mai yawan mutuwar aure a bayan Indiyawa a duniya. Ya zama wajibi ga dangin ma’aurata da su guji gutsuri-tsoma a cikin abin da bai kai ya kawo ba a cikin auren ’yan uwansu. Hakan ne zai kara masu mutunci da kima a wajen ma’auratan.

Jiddah Gaya Ƴar Jarida Ce Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum, Ta Rubuto Daga Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan