Ganduje Ya Naɗa Sarki Sanusi Shugaban Majalisar Sarakunan Kano

357

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da naɗin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a matsayin Shugaban sabuwar Majalisar Sarakunan Kano na farko.

Ba kamar yadda ake ta raɗe-raɗi ba cewa wata ƙila za a naɗa Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan, gwamnan ya zaɓi Sarki Sanusi II don ya zama Shugaban Majalisar Sarakunan na farko, muƙamin da za a sabunta shi bayan shekara biyu.

A makon da ya gabata, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartar da dokar da gwamnan ya sake gabatar mata don sake ƙirƙirar sabbin masarautu, bayan da Babbar Kotun Kano ta rushe masarautun, ta kuma sauke sarakunan.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya fitar ranar Litinin, Gwamna Ganduje ya umarci Sarki Sanusi da ya kira taron tattaunawa na Majalisar Sarakunan Kanon ba tare da ɓata lokaci ba.

“Bisa iko da Sashi na 4 (2) (g) da Sashi na 5 (1) (2) na Dokar Masarautun Jihar Kano ta 2019 suka ba Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, OFR, ya yi naɗe-naɗe kamar haka cewa: Maimartaba, Alhaji Muhammadu Sanusi II, Sarkin Masarautar Kano, a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano”, in ji sanarwar.

“Daga cikin mambobin Majalisar Sarakunan Jihar Kanon akwai dukkan Sarakuna Masu Daraja ta Ɗaya na Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya, Alhaji Aminu Ado Bayero, Alhaji Dakta Tafida Abubakar (Autan Bawo), Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar II da Alhaji Ibrahim Albdulkadir, waɗanda mambobin Majalisar Sarakunan ne kai tsaye, kamar yadda aka tanada a Dokar Masarautun Jihar Kano.

“Haka kuma, Sashi na 4 (2) ya bada sauran mambobi a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, shugabannin ƙananan hukumomi biyar, ɗaya daga kowace Masarauta, inda Fadar Sarki take.

“Sauran, kamar yadda Sashin ya tanada sun haɗa da Masu Naɗa Sarki guda (10), 2 daga Masarautun Biyar (5) da aka ambata a ƙarƙashin Sashi na 3 (1) na Dokar, Babban Limamin daga kowace Masarauta.

“Sauran mambobin sun haɗa da wakilin daga ‘Yan Kasuwa daga kowace Masarauta waɗanda Gwamna zai naɗa, kamar yadda Gwamna ya naɗa Alhaji Dalhat Al-Hamsad da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano a matsayin biyu daga cikin su.

“Haka kuma, Dokar ta yi tanadin cewa a matsayin mambobin Majalisar Sarakunan Jihar Kano, Gwamna zai naɗa wakili ɗaya daga Hukumomin Tsaro, ‘Yan Sanda, Jami’an Tsaro na Farin Kaya da Rundunar Tsaro ta Civil Defense. Da kuma wasu ƙarin sunaye da ba su gaza na mutum biyu ba da Gwmana zai naɗa, an naɗa Nasiru Aliko Koki a matsayin mamba a cikin Majalisar Sarakunan Jihar Kano, a wannan kaso. Sannan, Majalisar Sarakuna Jihar Kano ita za ta naɗa Sakataren Majalisar.

“Sashi na 5 (1), (2) na Dokar ya tanadi cewa, Shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Kano zai riƙa zagayawa ne a tsakanin Sarakuna Biyar (5) na Masarautun, kuma Gwamna da Shugaban Majalisar Sarakunan su ke da haƙƙin tabbatar da zagayawar shugabancin na tsawon shekara biyu (2) kawai.

“Naɗin zai fara aiki ne daga Litinin, 9 ga Disamba, 2019. An kuma umarci Shugaban Majalisar Sarakunan da ya kira taron ƙaddamar da Majalisar ba tare da ɓata lokaci ba kamar yadda tanade-tanaden Dokar suka buƙata.

“Gwamna Ganduje yana kira ga mambobin Majalisar da su yi kyakkyawan amfani da wannan dama da aka ba su wajen hidimta wa al’umma a jihar, kuma su ƙarfafa Masarautun da kuma tsarin shugabancin gargajiya a Jihar, su ba gwamnatin jihar shawara, musamman a kan harkokin tsaro”, a cewar sanarwar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan