Honarabul Abdulrahman Kawu Sumaila, haifaffen ɗan asalin ƙaramar Hukumar Mulki ta Sumaila ne da ke Jihar Kano wanda aka haifa a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1968.


Shekarun farko na rayuwarsa sun tafi ne ga neman ilimin kaɗaita Mahalicci kamar dai yadda al’ada da kuma tarbiyya irinta ‘ya’yan Musulmi ta tanada, inda ya yi karatu a matakan ilimin addini daban-daban.
Da yake masu magana sun ce ana bikin duniya akan yi na ƙiyama, Honarabul Kawu Sumaila ya soma gwamaya neman iliminsa da karatun boko a makarantar fumare ta Sumaila Gabas, inda ya samu takardar shaidar kammala karatun fumarae a shekarar 1976.
Daga nan sai Kawu Sumaila ya samu shiga makarantar sakandare ta Sumaila inda ya kammala a shekarar 1982 tare da samun sakamako mai inganci.
A shekarar 2001 kuwa, Honarabul Sumaila ya samu nasarar kammala karatunsa na difiloma a Jami’ar Bayero da ke Kano, haka kuma da yake masu magana na cewa kogi ba ya ƙin ƙari, Kawu Sumaila bai yi wani jinkiri ba wajen sake komawa Jami’ar domin ƙara zurfafa iliminsa, inda ya samu takardar shaidar babbar difiloma a shekarar 2003.
Cikin tarihin karatunsa ya nuna cewa Hon. Kawu Sumaila Ya Samu Digirin Farko akan harkokin addinin musulunci daga jami’ar karatu daga gida wato NOUN tare kuma da samun digiri na biyu akan harkokin mulki da gudanarwa daga jami’ar Bayero da ke Kano.
Duk dai a gwagwarmayarsa ta neman gishirin na zaman duniya, Honarabul Kawu Sumaila ya keta hazo inda ya halarci kwasa-kwasai iri-iri a ƙasashen Burtaniya da kuma Amurka, haka ma ya samu ƙwarewa da gogewa a fagen shata dokoki daga shahararrun jami’o’in nan da suka yi fice a duniyar ilimi, wato Jami’ar Harvard da ke ƙasar Amurka da kuma takwararta ta Oxford da ke Burtaniya.
A shekarar 1986 ne Honarabul Kawu Sumaila ya soma jefa ƙafarsa a fagen siyasa, ya taɓa zama memba a rusasshiyar jam’iyyar SDP a shekarar 1990, haka ma yana cikin jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar PDM ta wancan lokacin har ma ya taɓa zama ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar a tsakanin shekarar 1995 da 1997.
Ya taɓa neman kujerar shugabancin ƙaramar Hukumarsu ta Sumaila a inuwar rusasshiyar jam’iyyar UNCP kafin daga baya ya shiga jam’iyyar PDP inda har ya riƙe muƙamin jami’in jam’iyyar mai kula da harkokinta na kuɗaɗe a Jihar Kano, ya kuma yi takarar kujerar ɗan Majalisar Dokoki ta jiha mai wakltar mazaɓar Sumaila a Majalisar Dokoki ta Jihar Kano.
Ya taɓa zama memba a Hukumar kula da ɗakin Karatu ta Jihar Kano, haka nan kuma ya taɓa zama ko’o’dinetan shirin nan nan na rage raɗaɗin talauci da fatara a tsakanin al’umma, a hannu ɗaya kuma shugaban kwamitin duddubawa tare da sanya ido akan gudanarwar shi wannan shiri a yankin ƙaramar Hukumarsu ta Sumaila.
A shekarar 2003 ne Honarabul Abdulrahman Kawu Sumaila ya tsaya takarar ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya a karon farko domin wakiltar mazaɓar Sumaila da Takai.
Bayan da ya bar jam’iyyar PDP zuwa tsohuwar jam’iyyar ANPP, Kawu Sumaila ya shimfiɗa ingantaccen wakilci ga al’ummar mazaɓarsa waɗanda kafin zuwansa suke cikin maraicin rashin bakin faɗa a ji a matakin tarayya, wannan ne ma ya sa bayan cikar wa’adin wakilcinsa a shekarar 2007, sai bakin al’ummar mazaɓar ya zo ɗaya wajen sake lamunce masa karo na biyu inda suka sake zaɓensa a babban zaɓen watan Afrilun shekarar ta 2007.
Kasancewar masu magana na cewa ba a sayar da gaibu gobe a dawo, gamsuwa da salon wakilcin Honarabul Kawu Sumaila da jama’ar mazaɓarsa suka yi, tare da ɗimbin tarin tulin ribar dimokura]iyya da suka girba a sanadiyar wakilcinsa sai a shekarar 2011 ma, jama’ar ƙananan hukumomin Sumaila da Takai suka fito ƙwansu da gijensu suka ce yaba kyauta tukuici, domin haka suka yi tsayin da ka har sai da Honarabul Kawu ya sake komawa Majalisar Wakilai a karo na uku.
A wannan zangon ne ma tauraruwarsa ta ƙara ɗagawa sama’u bayan da aka zaɓe shi a matsayin Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisa.
Bayan da aka samu kafuwar jam’iyyar APC a ranar 6 ga watan Fabrairun Shekarar 2013, Kawu yana daga cikin waɗanda su ka nuna sha’awarsu wajen yin takarar gwamnan jihar Kano a shekarar 2015, sai dai wasu dalilai sun gaza bai ga nasarar lashe zaɓen fidda gwani ba.
Honarabul Kawu Sumaila ya rabauta da samun muƙamin mai baiwa shugaban ƙasa Shawara akan harkokin majalisa dokoki ta ƙasa.
A shekarar 2019 Hon. Kawu Sumaila ya yi takarar ɗan majalisar Dattawa a mazaɓar Kano ta Kudu, wanda aka yi wani mai kama da wasan kwaikwayo a matsayin zaɓen fiddo gwani.
Allah Cikin Ikonsa, Hon. Kawu ya shiga takarar majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar ƙananan hukumomin Sumaila da Takai, inda ya yi nasara da gagarumin rinjaye.
Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayar da gagarumar gudummawa a sassan rayuwar al’umma daban-daban, musamman abin da ya shafi samarwa matasa aiyukan yi. Fiye da mutum 100 ya Samawa aiyukan yi a gwamnatin tarayyar ƙasar nan.
Wani bincike da ƙungiyar Cigaban Matasan Kananan Hukumomin Takai Da Sumaila da su ka gudanar a shekarar 2018, sakamakon ya bayyana cewa babu wata ma’aikatar gwamnatin tarayya da Hon. Kawu bai samowa ɗan asalin Sumaila ko Takai aiki ba.
Bisa wannan ƙoƙarin ta sanya an sha karrama shi da lambobin yabo domin yabawa ƙwazo da ƙoƙarinsa tare da sadaukarwarsa wajen ganin al’ummar yankinsa sun samu ci gaba.
A shekarar 2006, marigayi Ɗan Isan Kano, kuma Uban Ƙasar Sumaila ya naɗa shi a matsayin Turakin Sumaila saboda gudummar da yake bayarwa ga mahaifar tasa. Haka ma a watan Satumbar shekarar 2012, Gwamnatin Tarayya ta zaɓo shi tare da ba shi lambar karramawa ta ƙasa ta OFR domin yabawa da ƙwazonsa.