Jami’an Tsaro Sun Kama Wani Gwamna Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa

420

An kama gwamnan Nairobi Babban Birnin Kenya Mike Sonko Mbuvi sakamakon zarginsa da aikata cin hanci da rashawa.


Mai gabatar da kara Noordin Haji da ya bayar da umarnin kama gwamna Mbuvi da wasu maikatan fadarsa 8 ya ce suma da dalilan kama su.


Ya ce ana zargin Mbuvi da wawure dala miliyan 3.5 mallakar gwamnati.


Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kenya ta gasgata kamen kuma ta ce an kama Mbuvi a lokacinda yake kokarin guduwa.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan