Mata Dubu Ɗari Takwas Na Fama Da Yoyon Fitsari A Ƙasar Nan

188

Hukumar Kula da Yawan jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mata 800,000 a ƙasar nan ke fama da matsalar yoyon fitsari, yayin da a kowace shekara ake samun 20,000 da ke kamuwa da matsalar.


Jami’ar hukumar da ke Kaduna, Mariama Darboe ce ta gabatar da wannan adadi na mata 800,000 da ke ɗauke da cutar yoyon fitsari a ƙasar nan, gabanin taron masu ruwa da tsaki kan matsalar da za’a fara ranar 18 ga wannan wata.


Darboe wacce ta bayyana adadin a matsayin mai tada hankali, ta ce ana samun tsakanin sabbin mata 12,000 zuwa 20,000 da su ke kamuwa da matasalar kowace shekara.


Jami’ar ta ce taron da za su gudanar zai taimaka wajen janyo hankalin hukumomi da sauran jama’a akan yadda ake kamuwa da cutar wajen gardamar haihuwa, wadda ke jefa dubban mata cikin halin kakanikayi, sakamakon rashin sani musamman ga waɗanda ke zama a kauyukan da ba’a samun kula da lafiyar su.


Darboe ta ce ana iya magance kamuwa da wannan matsala ta yoyon fitsari idan aka ɗauki matakan da suka dace ta hanyar jinkirta ɗaukar ciki ga ƙananan mata da samun kula daga ƙwararrun masu karɓar haihuwa da kuma baiwa matan da ke fuskantar matsalar haihuwa kular da ta dace.

Rahoton Rfi Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan