Shugaba Buhari Zai Tafi Ƙasar Masar

198

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi garin Aswan na ƙasar Masar ranar Talata domin halartar wani taron zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka.

Kamar yadda fadarsa ta bayyana a shafinta na Twitter, shugaban zai shafe ranakun Alhamis da Juma’a yayin taron.

Ta kara da cewa taron, wanda aka kira shi da suna “An Agenda for Sustainable Peace and Development in Africa”, wani yunkuri ne da nahiyar Afirka take yi na nemo wa kanta hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro da kuma cigaba.

Wannan ne balaguro na 12 zuwa wajen Najeriya da Buhari zai yi tun bayan cin zabensa a karo na biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan