Da Yiwuwar Gattuso Ya Maye Gurbin Anceloti

172

Akwai yiwuwar tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta A.C Milan wato Gennaro Gattuso ya maye gurbin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Napoli wato Carlos Anceloti.

Hakan ya biyo bayan tuntubar da mahukuntan kungiyar ta Napoli suka yiwa Gattuso.

Ayanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Napoli suna samun koma baya a gasar Serea A ta kasar Italia.

Ayau dai Napoli zasu buga wasan zakarun nahiyar turai da kuma kungiyar kwallon kafa ta Genk inda Napoli ke matsayi na biyu a rukunin da maki 9.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan