Dattijo Ɗan Shekara 74 Ya Angwance Da Masoyiyarsa ‘Yar Shekara 82 A Kano

292

A jihar Kano, wani dattijo ɗan shekara 74, Muhammadu Liti ya auri masoyiyarsa ‘yar shekara 82, Fatima Malam bayan sun shafe kimanin wata takwas suna soyayya.

An ɗaura auren ne ranar Talata da safe a unguwar Kan Faƙo dake Ɗorayi, a cikin ƙwaryar birnin Kano, kamar yadda wani rahoton Freedom Radio da jaridar KANO FOCUS ta bibiya ya tabbatar.

Mista Liti ya biya sadakin N10,000 ga Miss Malama, wadda ke sana’ar soya ƙosai da wainar rogo a yankin.

Amaryar, wadda ta bayyana farin cikinta bisa samun abokin rayuwa, ta ce an ɗaura wannan aure ne a kan tsantsar soyayya.

Amaryar, Fatima, ta ce za ta yi biyayya ga angonta ɗan shekara 74, duk da cewa ta girme shi da shekara takwas.

“Farin cikin da nake ji yau kamar na alhajin da zai je Maka ne”, in ji ta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan