EFCC Ta Fara Bincikar Abdulaziz Yari Akan Satar Naira Biliyan 900

143

Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’anati wato EFCC, ta bayyana cewa a yanzu haka tana gudanar da bincike akan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari bisa wasu kuɗin kwangila naira biliyan 900 da suka yi ɓatan dabo a gwamnatinsa.

Shugaban hukumar reshen jihar Sokoto, Abdullahi Lawal ne ya bayyana haka a lokacin zagayen wayar da kai domin tunawa da ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta duniya da ya gudana a jihar Sokoto

Wani rahoto da Jaridar ThisDay ta ruwaito ya bayyana shugaban hukumar yana cewa waɗannan makudan kuɗaɗe da ake tuhumar Yari akansu an fitar da su ne da nufin gudanar da kwangiloli daban daban, amma kuma ba’a gudanar da kwangilolin ba kuma babu kuɗin.

A wani ɓangaren kuma Abdullahi Lawal, ya ce tun lokacin da aka buɗe ofishin hukumar EFCC a Sakkwato sun samu ƙararraki guda 236, in da su ke binciken guda 151, sun gabatar da guda 20 a gaban kotu, yayin da sun samu nasara a guda 4.

Ya kara da cewa sun kuma ƙwato zambar kuɗi naira miliyan 910, sun kai naira miliyan 125 zuwa babban bankin ƙass domin ajiya, sa’annan sun ƙwato manyan motocin alfarma guda 4 da keke napep 53.

A ƙarshe ya ce a yanzu haka suna binciken wani ɗan kwangila a jihar Zamfara da aka bashi aikin gina famfon tuƙa-tuƙa guda 287 akan kuɗi naira biliyan 200 tun a cikin shekarar 2013, amma bai yi aikin ba, haka zalika suna binciken wani Sanata daya ci bashin naira miliyan 400 da sunan zai tayar da komaɗar kamfanin masaka na Hirjira, amma shiru kake ji.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan