Sarkin Kano Sanusi II Ya Halarci Taron Sarakunan Arewa A Kaduna

426

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II ya halaci taron sarakunan arewa karo na Shida (6) wanda aka gudanar a garin Kaduna.

Taron Sarakunan wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, an gabatar da shi ne a babban ɗakin taro na gidan Arewa wato Arewa House

Sarakunan sun tattauna batutuwan da su ka shafi tsaro tare da cigaban ƴankin arewacin ƙasar nan.

Tun da farko dai taron ya samu halartar mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hajia Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mai masaukin baƙi, in da ta wakilci gwamna Malam Nasiru el-rufa’i.

Sai dai kuma ba’a ga fuskokin Sauran sababbin Sarakunan Kano ba, waɗanda su ka haɗa da Sarkin Bichi da Sarkin Rano da kuma Sarkin Ƙaraye da na Gaya, duk da majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar da ta mayar da su Sarakuna masu daraja ta ɗaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan