Sarkin Rano Tafida Abubakar Ilah Ya Ƙaddamar Da Majalisar Masarautarsa

690

Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Dakta Tafida Abubakar Ilah II ya ƙaddamar da majalisar masarautarsa, tare da yin zaman farko da wannan majalisa a fadarsa da ke Rano.

Cikin wata Sanarwa da sakataren yaɗa labarai na masarautar Wali Ado Rano ya sanyawa hannu tare da rabawa manema labarai.

Sanarawa ta ƙara da cewa ƙunshin masarautar yana ɗauke da sunayen mutane waɗanda su ka haɗa da:


Alhaji Ɗan Lami Ahmed Rano da Farfesa Abdu Salihi Kibiya da kuma Isa Ahmed T/Wada da Alhaji Garba Adamu Sumalia, da Ustaz Ɗayyabu Umar Me Mai Rano sai kuma Honarabul Ubale Bompai.

Zaman majalisar na farko ya ƙunshi shugabannin ƙananan hukumomi da su ke wannan masarauta tare da babban limamin juma’ah na Rano wato Malam Kabiru Sani.

Wannan dai yana zuwa kwana biyu da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a matsayin shugaban majalisar Sarakunan jihar Kano.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan