Ƙungiyar Ma’aikatan Lantarki Sun Garƙame Ofishin KEDCO

176

Ƙungiyar ma’aikatan dake samar da wutar lantarki ta kasa ta tsunduma a yajin aikin sai baba ta gani a yau.

Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan dake Samar da wutar lantarki ta kasa shiyar arewa maso yamma kwamared Muhammad Musa, ne ya bayyana haka ya yin da yake zantawa da manema labarai a yau.

Kwamared Muhammad Musa, yace sun dauki matakin ne sakamakon Gaza biya musu bukatun su da kamfanonin da suke yiwa aiki su.

Ya kuma ce akwai ma’aikatan da suka bar aiki sama da dubu biyu wanda har ya zuwa yanzu an gaza biyan su hakkokin su na barin aiki duk da cewa sun mika korafe-korafen su ga ministan samar da wutar lantarki na kasa.

Rahoton Freedom Radio, Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan