Jami’an Kwastam Sun Harbi Wani Ɗalibin Jami’a A Kano

494

Ana zargin wasu jami’an Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS, da raunata wani ɗalibi mai karatun digiri na biyu a ƙafafuwansa lokacin da suka yi harbi motarsa.

Majiyarmu ta gano cewa ɗalibin, Jibrin Yahya Maikifi yana kan hanyar dawowa Kano ne daga Gashuwa ta jihar Yobe, ranar Litinin, lokacin da Jami’an na Kwastam suka tsayar da shi a Zakirai dake Kano.

Mista Makarfi, wanda ya yi magana daga gadon asibiti, ya ce Jami’an na Kwastam sun harbi motar ne bayan ya yi tsayuwar gaggawa.

A ta bakinsa, jami’an ba sa sanye da kaki, kuma ba su sa wata alamar tsayawa a hanya ba.

Mista Makarfi, mai karatun digiri na biyu a Computer Engineering a Jami’ar Gabashin Landan, ya yi zargin cewa Jami’an na Kwastam sun arce da gudu a cikin motarsu lokacin da suka lura cewa sun ji masa rauni.

To, sai dai Mai Magana Da Yawun Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, na Rundunar Kano da Jigawa, Isa Danbaba ya ce har yanzu rundunar ba ta tabbatar da afkuwar al’amarin ba.

Mista Danbaba ya ce rundunar na kan binciken al’amarin, saboda akwai Jami’an Kwastam har kashi uku dake aiki a yankin.

“Akwai Sashin Gwamnatin Tarayya, sashi na musamman da kuma Rundunar Yanki ta Kano da Jigawa”, in ji shi.

Amma Mai Magana da Yawun Rundunar ya ce muggan mutane za su iya yin ɓadda-bami a matsayin Jami’an Kwastam su aikata laifuka.

Ko a ranar Laraba da ta gabata, wani sajan ɗan sanda dake aiki a bankin UBA dake Malam Kato Square a Kano ya harbe Mus’ab Mubammad har lahira, wani ɗalibi ɗan shekara 21 wanda ya kammala karatun digiri na farko a Computer Science daga Noida International University, India.

Sai dai Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce rundunar za ta gurfanar da ɗan sandan gaban kotu idan sun kammala binciken dalilan da suka haifar da kisan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan