Masarautun Kano: Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Martani Ga Umarnin Kotu

304

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani ga hukuncin wucin gadi da Babnan Kotun Kano ta yanke, inda ta dakatar da Gwmana Abdullahi Umar Ganduje daga ƙwace ikon masu naɗa sarki na Masarautar Kano kamar yadda Dokar Masarautun Kano ta 2019 ta tanada.

Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne masu naɗa sarki, Madaki, Makama, Sarkin Dawaki Maituta da Sarkin Bai suka garzaya Babbar Kotun Kano inda suke roƙon kotun ta yi hukuncin wucin gadi da zai hana Gwamnan Ganduje ƙwace aikace-aikace da ikon masu naɗa sarki na tale-tale bisa sabuwar “Dokar Masarautun Kano ta 2019”, har lokacin da za a kammala sauraron ƙara.

Hukuncin wucin gadi na biyu da nasu naɗa sarki ke roƙon kotun ta yi shi ne ta hana Gwamna Ganduje ɗaukar kowane irin mataki ko na kawar, tumɓuke ko sauya wa Sarkin Kano wajen aiki ba tare da tuntuɓar su ba.

A ranar Talata, kotun, wadda Mai Shari’a A.T Badamasi ke jagoranta, ta yanke hukuncin na wucin gadi inda ta hana Gwamna Ganduje ƙwace aikace-aikace da ikon masu naɗa sarkin tun na tale-tale.

Amma Mai Shari’a Badamasi bai amince da buƙatar masu ƙara ta biyu ba.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, ya ce wancan hukunci bai shafi kasancewar sabbin Masarautun ba.

Ya ce wannan wata farfaganda ce da masu sukar ƙirƙirar sabbin Masarautu ke yi, kuma za su kunyata lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe.

Sanarwar ta tabbatar da cewa hukuncin da kotun za ta yanke zai daɗaɗa wa gwamnatin jihar Kano duba da yadda aka bi ƙa’ida wajen kafa sabuwar dokar Masarautun.

Kwamishinan ya yi kira ga al’umma a jihar da su nutsu, kuma su ci gaba da bin doka da oda yayinda kotun ke shirin yanke hukunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan