Aikin ɗan sanda a ƙasarmu ta gado (Najeriya) da Turawan mulkin mallaka na ƙasar Birtaniya suka kafa shi a yau kusan shekaru 200 da suka gaba ta (1820), domin kare manufofinsu na mulkin mallaka, kuma suka faro daga cikin yankin da yau ake kira jihar Imo a Kudu Maso Gabashin Najeriya yana buƙatar gagarumin sauyin fasali domin ya tafi daidai da zamanin da ake ciki a yau, wanda kuma hakan ba zai taɓa samuwa ba har sai gwamnatin sama (Federal) ta yi abin da yakamata, sannan ba zai taɓa samun martaba da kima a idon jama’ar ba har sai ‘ya’ya masu asali da martaba da nagarta sun shiga cikinsa.
Ba yadda za a yi aikin ɗan sanda a Najeriya ya sa mu nasara da matuƙar ana ɗibar ‘ya’yan da suka taso cikin rashin kyakkyawar tarbiyya, cikin miyagun ayyuka da rashin da’a.
Aikin ɗan sanda yana buƙatar mutane ne masu gaskiya, ɗa’a, amana, tausayi, iya mu’amala da jama’a, illimi, tsoron
Allah da kuma kyawawan ɗabi’u waɗanda ba a samun su sai a gidan da aka gina tubalinsa da gaskiya da tsoron Allah.
Ta yaya za a wayi gari a ce matashin da bai ɗauki cin amana komai ba, kuma bai ɗauki kunya a matsayin abu mai kyau ba, mara ɗa’a da tarbiyyar gida kuma mara da’a a cikin al’umma, a ɗauki kayan aikin ɗan sanda a ba shi, sannan a yi zaton samun sakamako mai kyau? A yi zaton cewa ba zai ɓoye gaskiyar mai gaskiya ba? Ba zai hallaka wanda bai cancanci hallakawa ba? Ba zai karɓi cin hanci ba?
Aikin ɗan sanda muhimmin aiki ne da ya ke buƙatar mutane masu kyawawan halaye da da kyakkyawar tarbiyya kuma jarumai, domin dokar da ta kafa aikin ta tabbatar da cewa ‘yan sanda, baya ga aikinsu na ‘yan sanda, suna kuma iya yin ayyukan soja idan buƙatar hakan ta taso wa ƙasa.
Aikin ɗan sanda yana bukatar goyon bayan gwamnatin ƙasa da na jihohi da ƙananan hukumomi da kuma al’ummar ƙasa baki ɗaya, kuma har sai gwamnatin ƙasa da al’ummar ƙasa sun bai wa aikin goyon baya ɗari bisa ɗari (100%), kafin ya zama mai martaba da kima kuma abin yarda ga kowa, kuma hakan zai samu ne ta bai wa aikin damar cin cikakken ‘yanci da samar wa aikin dukkan kayan aiki na zamani da ake buƙata, kuma waɗanda za su yi aiki da kayan (‘yan sandan) su zama abin amincewa a cikin al’umma, domin matukar aka bar maganar saɓanin: addini aƙida, ƙabilanci da yanki suka shiga cikin aikin ɗan sanda, babu inda aikin zai je face kullum jiya a yau.
Ya Allah Ya tsarkake wannan aiki na ɗan sanda daga dukkan miyagu da azzalumai masu ɓata wa wannan muhimmin aiki suna, Ya Allah, Ka cusa wa hukumomi tausayawa wannan aiki har su kawo cikakken sauyi a cikinsa, kuma mutane nagari amintattu masu gaskiya da amana su mamaye kowane ɓangare na aikin, Ka kuma sanya wa jama’ar ƙasa yadda da ƙaunar jami’in ɗan sanda da ake yi wa kirari da: “ƊAN SANDA ABOKIN KOWA.”
Yusuf Yau Rano