Sarkin Rano Tafida Abubakar Ilah Ya Kai Ziyara Gidan Gyaran Hali Da Ke Rano

381

Mai martaba Sarkin Rano Alhaji Dakta Tafida Abubakar Ilah ya kai ziyara babban gidan gyaran hali da tarbiyya da ke garin Rano.

Sarkin ya kai wannan ziyarar ne a ƙoƙarinsa na ganin ya bayar da gudummawa tare da yin jan hankali ga waɗanda ƙaddarar zama ta kai su ga zama a wannan gida na gyaran hali.

Tun da farko Sarkin ya samu tarba ta musamman daga jami’an gidan, in da aka fito da mazauna gidan gaba ɗayansu, in da Sarkin ya yi musu nasiha tare da jan hankalinsu akan da su zama mutanen kirki waɗanda al’umma za ta yi alfahari da su.

Haka zalika Sarkin ya yi musu addu’ar gama zaman da su ke lafiya tare kuma da fatan samun tarbiyya abar kwatance.

A ƙarshe Sarkin ya ba su talllafin Katifu da Tabarmi da Barguna da abubuwan da za’a zuba ruwa da kuma sauran abubuwan da su ke amfani da shi a gidan gyaran tarbiyya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan