Wata matashiya ‘yar shekara 16 ta fada rijiya kwana daya kafin ranar daurin aurenta a garin Gajaja na karamar hukumar Dambatta da ke jihar Kano.
Matashiyar mai suna Fadima ta gamu da ajalinta ne yayin da suka je gidan mawankiya tare da kawayenta, inda a nan ne ta fada rijiya bisa rashin sani.
Kanin angon marigayiyar ya shaida wa BBC cewa suna tsaye a gidan mawankiyar sai kawai ta zame ta afka cikin rijiyar.
Mahaifiin Fadima Alhaji Abubakar ya shaida wa BBC cewa yau Alhamis ce aka shirya daura mata aure da angonta amma sai kaddara ta dauke ta.
“Auren soyayya ne, ita tana so shi ma yana so. Yanzu haka ma ‘yan biki ne dankam a wurin zaman makoki,” in ji Alhaji Abubakar.
Ya kara da cewa yanzu suna kokarin shawo kan Hajiya Lami, wadda ita ce mawankiyar da abin ya faru a gidanta sannan kuma kanwa ga mahaifiyar amaryar, domin kuwa ko abinci ta kasa ci.
BBC ta samu jin ta bakin Lami, inda ta ce tsautsayi ne ya faru wanda kuma ba ya wuce ranarsa.
Kanin angon mai suna Labaran ya ce iyayen amaryar mazauna garin Babura ne na jihar Jigawa, kuma Fadima ta je garin Dambatta ne a shirye-shiryen bikin nata.
Angon marigayiya Fadima bai iya yin magana ba saboda halin alhini da yake ciki.
Rahoton BBC Hausa
