Auren Wuri Yana Kare Haɗarin Kamuwa Da Cutar Ƙarin Mahaifa – Likitoci

1356

Likitoci a ɓangaren haihuwa sun bayyana cewar auren wuri yana hana kamuwa da ciwon karin mahaifa. Wani babban likitan mata a birnin Ikko Dakta Gabriel Akilo ne ya bayyana hakan a wajen wani taron karawa juna sani karo na 9 daya gudana a jihar Lagos.

Dakta Akilo ya ce cutar tana kama mata ne lokacin da shekarun su suka tura batare da haihuwa akai akai zamanin budurci ba.

Likitan ya ce binciken su ya gano cewar auren wuri, da kuma haihuwa a lokutan ƙuruciya yana ƙarawa mahaifa lafiya, idan kuma girma ya fara kama su kuwa akwai buƙatar su huta, a cewar sa.

Akwai bukatar mu tattauna wannan babbar matsala dake fantsama kamar wutar daji, ciwon na karin mahaifa yana yawaita a tsakanin mata ne yan shekaru 35 zuwa 45.

Ko da ya ke likitan ya ce zai yi wuya a samu ƴan ƙasa da shekaru 20 da wannan lalurar, a saboda haka yake shawartar mata su rungumi auren wuri domin samun lafiyar jiki da ta ciki domin kawar da cutar a ƙasar nan.

“A ganin sa ba wani abu ne ke hana matan auren na wuri ba illa ruwan ido, da ya ce a nan ne su ke jifan gafiyar ɓaidu wajen asarar maza nagari.”

Dakta Akilo ya bukaci iyaye su karfafawa yayan su mata gwiwar auren wuri domin kawar da lalurar ƙarin mahaifa a tsakanin al’umma.

Daga nan likitan ya ja hankalin mata game da magunguna da suke sha domin samun sauƙin cutar, gudun kaucewa rasa idanu a wajen neman gira. Ya ce wasu magungunan su kan illata ƙoda, mafitsara, ƴaƴan hanji da dukkanin ɓangarori da ke taimakawa ƙwaryar ciki.

Rahoton Dala FM Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan