Direbobin A Daidaita Sahu A Kano Sun Fasa Tafiya Yajin Aiki

409

Ƙungiyar Direbobin Babura Masu Ƙafa Uku na A Daidaita Sahu sun fasa tafiya yajin aiki na kwana ɗaya da suka shirya farawa, bayan cimma matsaya da gwamnati.

Majiyoyin ta ruwaito cewa direbobin sun sanar da shirin tafiya yajin aiki a ranar Juma’ar nan sakamakon “yawan haraji”.

Amma, Shugaban Ƙungiyar Direbobin Babura Masu Ƙafa Uku na A Daidaita Sahu ta Jihar Kano, TOAKAN, Sani Sa’idu-Dankoli, ya ce sun cimma matsaya da Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA.

“Mun yadda za mu biya kuɗin rijista N8,000, amma maganar harajin N18,000 na shekara-shekara za a ajiye ta zuwa 2020”, in ji shi.

Mista Sa’idu-Dankoli ya ce za su tattauna da KAROTA domin ta ba su damar biyan harajin a hankali a hankali.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan