Kafa Majalisar Sarakuna Ba Sabon Abu Ba Ne A Kano – Ganduje

159

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Gandije ya ce matakin da gwamnatin sa ta dauka na kirkiro sabuwar majalisar masarautu a jihar ba sabon abu ba ne a duk inda ake da sarki fiye da daya, duk kuwa da cece-kucen da jama’a ka yi.


Ganduje ya ce a da can lokacin tsohuwar jihar Kano akwai irin wannan hukumar da ta kumshi masarautun Kano, Kazaure, Gumel da Hadeja.


“Aikin hukumar shi ne su dinga zama lokaci zuwa lokaci, su bada shawarwarin a kan al’amuran da suka shafi al’ummarsu ko kuma wani abu da gwamnati ta fito da shi.

Musamman ma yanzu da aka fito da shirin ba da ilimi kyauta na dole, akwai bukatar shigowar sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki, domin gwamnati kadai ba za ta iya ba.”


To sai dai rahotanni sun bayyana cewa, babbar masarautar Kano ta ce bata sami rubutaccen sako daga gwamnati ba dangane da kafa majalisar, da kuma ayyana Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a zaman shugaban ta na farko.


A cikin hirar shi da Sashen Hausa, Gwamna Ganduje ya ce tuni da aka aikewa masarautar rubutaccen sako dangane da hakan.


“An riga an kai wannan takarda, kuma sun sa mana hannun cewa sun karbi takardar, saboda haka muna sauraren amsa daga wajensu.” In ji Gwamna Ganduje.


Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da babbar kotun jihar Kano ta bada umarnin dakatar da kaddamar da majalisar sarakunan, sakamakon karar da masu nadin sarki a Kanon suka gabatar mata, inda suka bukaci ta dakatar da gwamnatin jihar daga kaddamar da majalisar.

Rahoton VOA Hausa

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan