Wasu rahotanni sun ruwaito mai dakin shugaban ƙasa Muhammad Buhari Aisha ta bayyana haka ne yayin da take tattaunawa da gidan talabijin na TVC, inda tace a yanzu basu samun kadaicewa ita da shugaba Buhari kamar yadda aka san ma’aurata suke yi saboda sha’ani irin na mulki.

Wannan dalili yasa Aisha Buhari tace shi yasa take maganganu tare da bara a kafafen sadarwa. Sai da da aka tambayeta shin bata samun daman tattauna wadannan matsalolin da Buhari a duk lokacin da suka kadaice?
Sai tace “Ai bamu da lokacin kadaicewa da juna a fadar gwamnati Aso Rock Villa, hatta a cikin dakinmu kuwa ba ma iya kadaicewa da juna.” Aisha ta kara da cewa yawan kula da sha’anin mulki ya hanasu lokacin daya kamata suna kwashewa a matsayin mata da miji.
Sai dai tace da a ce duk ministocin shugaba Buhari da hadimansa za su dage wajen sauke nauyin dake wuyansa yadda ya kamata, toh da ita da mijinta sun huta, kuma da ba ta dinga fita tana babatu a kafafen watsa labaru ba.
“Babu wani lokacin kebewa a Villa, saboda kullum muna cikin aiki ne kawai, muna samun rahotanni iri iri daban daban, ina tunanin mutanen da ya nada a gwamnatinsa su tashi tsaye su yi abin da ya kamata, shi yasa siyasar ubangida ba shi da kyau.
“Dole sai mun sa mutanen da suka cancanta a inda suka cancanta domin mu huta, wannan ne kadai zai sa uwargidar shugabankasa ta daina magana.” Inji Aisha.
[…] Muƙalar Da Ta GabataBa Ni Da Ikon Keɓewa Da Mijina – Aisha Buhari […]