Home / Labarai / An Gano Cutar Da Ke Sanya Shugabannin Ƙasar Nan Satar Kuɗin Al’umma

An Gano Cutar Da Ke Sanya Shugabannin Ƙasar Nan Satar Kuɗin Al’umma

Wani masanin halayyar dan adam kuma likitan masu taɓin hankali Farfesa Ernst Josef Franzek ya bayyana cewa wani nau’in hauka ne ke sanya shuwagabannin ƙasar nan ɗabi’ar satar kuɗaɗen al’umma.


Farfesa Franzek wanda ya kwashe shekaru 40 yana bincike a fannin hankali da kwalkwalr dan Adam, ya kasance baturen ƙasar Jamus.

Da ya ke amsa akan dalilin da ya sa shugabannin ƙasar nan ke sata, sai ya ce

“Attajirai a Najeriya suna samun kuɗi, amma ƙwaƙwalwarsu ta mutu, su kuma talakawan basa iya furta ra’ayinsu har ya yi tasiri.”


Farfesan ya ƙara da cewa wannan matsalar da al’ummar ƙasar nan su ke girma a ciki, da ace shugabannin ƙasar nan na samun tarbiyya yadda ya kamata, kuma ace sun girma cikin yanayi mai kyau, toh da ba su saci kuɗaɗen jama’a ba.

Farfesa Franzek ya ce idan yaro tun yana ƙarami ya saba da cewa sai ya wahala kafin ya samu abincin da zai ci, ko kuma sai ya nema da kansa, sakamakon iyayensa basu da halin bashi kudi, to dole irin wannan yaro yayi sata idan ya zama shugaba, saboda ƙwaƙwalwarsa ta saba da haka.


Wannan cuta dai sunan ta a turance ‘Kleptomania’, wanda ba ta barin mutum ya samu kwanciyar hankali muddin bai saci kayan mutane ba.


A ƙarshe Farfesan ya ba da shawarar yadda za’a sauya al’amarin, in da yace ya zama wajibi al’ummar su fara zaɓen shugabannin masu kyawawan manufofi.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *