Ba Da Sana’ar Fim Kawai Na Dogara Ba – Aisha Tsamiya

481

Fitacciyar Jarumar Finafinan Hausa A’isha Aliyu Tsamiya, tana ɗaya daga cikin jarumai mata ‘yan fim da suka halarci aikin umarah a ƙasa mai tsarki a bana.

Jarumar dai ita ce wadda ta ɗauki nauyin ƙayataccen shirin nan mai suna “KALAN DANGI” wanda ya fita kasuwa a shekarar da ta gabata.

Jarumar, wadda yanzu ta ɗan dakata fitowa a Finafinan Hausa, hakan yasa ake ganin kamar ta rage samun kuɗi har ma wasu suna tambayar wai da wane Kuɗi ta je aikin Umarah?

Mun tattauna da jarumar a lokacin da ta ke ƙasa mai tsarki wurin ibadah.

Bayan sun yi mata fatan alheri, sai kuma suka tambayeta a kan wai mutane na tambayar da wane kuɗi ta je aikin Umarah kasancewar ta rage fitowa a cikin Finafinan Hausa.

Sai jarumar ta ce: ” Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) game da tambayar da aka yi min ni dai na kasance ba wai ga harkar fim kawai na dogara ba.

Ina yin Sana’oi na saye da sayarwa kayan da na ke sayowa a ƙasar waje. Ko iya kasuwancin saye da sayarwa ɗina na riƙe ya ishi su biya mani buƙatuna na yau da kullum.

Don haka ya kamata jama’a su sani ba wai ga fim kawai na dogara ba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan