Buhari Ya Fi Duk Shugabannin Najeriya Girmama Dimokuraɗiyya- Yahaya Bello

311

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ga baiken matakin da jaridar Punch ta ɗauka na ci gaba da kiran Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin ‘mai mulkin kama-karya’, wanda ya fake da dimokuraɗiyya.

Gwamna Bello, wanda ya tattauna da manema labarai na Fadar Gwamnatin Tarayya dake Abuja ranar Alhamis, ya ce bai taɓa ganin wani tsohon shugaban mulkin soja da ya juye ya zama ɗan siyasa mai girmama dimokuraɗiyya ba kamar Shugaba Buhari ba a tarihin siyasar Najeriya.

A ta bakinsa, duk wanda ya kira Shugaba Buhari a matsayin mai kama-karya, shi ne yake son ya zama mai kama-karya.

“Shugaba Buhari shi ne shugaban ƙasa da ya fi girmama dimokuraɗiyya wanda na taɓa gani. Wannan shi ne karon farko da muke ganin tsohon shugaban mulkin soja wanda yake bin tafarkin dimokuraɗiyya ya bar abubuwa suna faruwa a mahaifarsa a tafarkin dimokuraɗiyya, ba a ma yi maganar abubuwan da suke faruwa a ƙasa ba.

“Duk wanda yake kiran sa a matsayin mai kama-karya, ina jin wannan mutumin shi ne yake so ya zama mai kama-karya, ba Shugaban Ƙasa ba”, in ji gwamnan.

Da yake mayar da martani ga rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, NBS, wanda ya yi iƙirarin cewa Kogi ita ce jihar da tafi kowace jiha talauci a Najeriya, gwamnan ya ce jiharsa ita ce jihar da aka fi yabo a ƙasar nan.

A cewarsa, gwamnatinsa ta yi abubuwa da dama don tabbatar da yin abubuwa a fili, abinda ya ce ya haɓaka tattalin arziƙin jihar.

“Kun ga, ya kamata ku duba ku karanta abinda wancan rahoto ya ƙunsa filla-filla kafin ku iya yin hukunci. Kun ga, bai kamata kawai mu saurari wani, mu faɗi abinda ya faɗa ba daidai ba.

“Kamar yadda na faɗa, a da a jihar Kogi, a ma’aikatan gwamnati, kafin ka zama Babban Sakatare, sai ka biya maƙudan kuɗaɗe, amma yanzu za ka zama ne bisa cancanta.

“Kafin ka zama shugaban ƙaramar hukuma, ko kuma bari mu ɗauke shi ta ɓangaren siyasa, ni ne jagoran APC a jihar Kogi, ba wani mutum da ya samu fom ko ya zama ko ma me ya zama, da zai yi iƙirarin biyan ko yake iƙirarin ya biya wani abu ga wani shugaban siyasa.

“Sakamakon toshe ƙofofi da kuɗaɗe ke zirarewa da muka yi, mun iya ƙara yawan kuɗaɗen shigar jihar Kogi daga miliyan N300 zuwa fiye da biliyan N1 a duk wata.

“Idan kuka duba kason, za ku iya yin hukunci. To, idan wani ya ce jihar Kogi ita ce jihar da tafi kowace jiha cin hanci, to fa bayanan wannan mutumin na kuskure ne.

“Jihar Kogi ita ce jihar da aka fi yabo a ƙasar nan, kuma ta tashi tsaye don yaƙi da cin hanci saboda muna amfani da ɗan abinda muke da shi wajen ciyar da jihar gaba da kuma yaƙi da rashin tsaro.

“Da cin hancin ya kai yadda ake faɗa, haka ba za ta faru ba”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan