Ganduje Ya Sanyawa Sabuwar Gada Sunan Sheik Ƙariballah

255

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanyawa sabuwar gadar da ake aikin gininta a kan titin kasuwar Rimi sunan shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika Sheikh Kariballah Sheikh Nasiru Kabara.

Gwamna Ganduje ya bayyana radin sunan sabuwar gadar ne a yau, a yayin da ya ke jawabi wajen taron Maukibi da mabiya darikar Kadiriyya ke shiryawa a duk shekara.


Gwamna Ganduje ya ce gwamnati ta yi la’akari da irin gudunmawar da Sheikh Kariballah ke bayarwa wajen daukaka addinin musulunci da kuma hadin kan jama’a, shine ma dalilin da ya sanyawa wannan sabuwar gadar sunanasa.

Gwamna Ganduje ya kuma bukaci Sheikh Kariballah da ya ziyarci gurin da ake aikin ginin gadar don ganewa idanun sa yadda aikin yake wakana tare da sanyawa aikin albarka.

Maukibin wanda Sheikh Muhammd Nasiru Kabara ya assasa lokacin yana raye, ya fara shi ne da mutane 40, a yanzu kuma ɗaruruwa ne ke halartar taron daga jihohin ƙasar nan da wasu daga cikin ƙasashen ƙetare.

Rahoton Freedom Radio, Kano

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan