Ina Roƙon Mahukunta Da Su Magance Matsalar Satar Yara – Sheikh Ƙariballah Nasiru Kabara

276

Shugaban ɗarikar ƙadiriyya na Afrika Sheikh Dakta Ƙaribullah Nasiru Kabara ya yi kira ga Shugabanni da su mayar da hankali wajen magance matsalolin sace-sacen yara da matsalolin fashi da makami maimakon su zauna suna abubuwan da ba su kamata ba wanda hakan wajibi ne a kansu.

Sheikh Ƙariballah Nasiru Kabara ya bayyana hakan a lokacin da ya ke wata tattaunawa da manema labarai a lokacin da ya ke shirin fitowa domin tafiya filin Maukibi da mabiya ɗarikar ƙadiriyya ke gudanarwa a yau, ya nemi shugabanni da su mayar da hankali wajen magance matsalolin rashin tsaro dake addabar faɗin ƙasar nan.

Sheikh Ƙaribullahi ya yi kira ga mahukunta akan idan an kama masu laifi yana da kyau a rinka gurfanar dasu a gaban shari’a domin yanke musu hukunci, wanda hakan zai taimaka gaya wajen rage aikata laifuka musamman ta ɓangaren shaye-shaye da sara suka.

A yau Asabar ne ake gudanar da maukibin Ƙadiriyya karo na 69 wanda mabiya ɗarikar ke yi a duk shekara da nufin tunawa da ranar haihuwar Sidi Abdulkadir Jilani.

Maukibin wanda Sheikh Muhammd Nasiru Kabara ya assasa lokacin yana raye, ya fara shi ne da mutane 40, a yanzu kuma ɗaruruwa ne ke halartar taron daga jihohin ƙasar nan da wasu daga cikin ƙasashen ƙetare.

Rahoton Freedom Radio Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan