Ina Nan Da Rai Na Ban Mutu Ba – Janaral Babangida

1630

Tsohon Shugaban ƙasa a mulkin soja Janaral Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya ba kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai na BOGI su ka rawaito mutuwarsa ba.

Janaral Babangida ya bayyana hakan a shafinsa na fasebuk, in da ya ce lafiyarsa ƙalau, batun mutuwarsa kuwa ƙarya ce tsagwaronta.

Tun da farko dai wasu shafukan BOGI ne su ka rawaito mutuwar tsohon shugaban ƙasar.

Idan za’a iya tunawa dai ko a cikin watan Mayun shekarar nan sai da aka samu irin wannan rahoton.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan