A yau za a fafata wasa mai zafi a gasar ajin Firimiya ta kasar Ingila tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da Manchester City.
A makon daya gabata dai Manchester City sun sha kashi a hannun abokiyar hamayyarsu wato Manchester United har gida daci 2 da 1 inda hakan ya ja musu Liverpool tayi musu tazarar maki 14.

Ita kuwa Arsenal a makon daya gabata ta sha da kyar a hannun West Ham United daci 3 da 1 ta hannun mai horaswarta na rikon kwarya, amma kafin haka Arsenal sun fafata wasanni da dama batare da sunyi nasara ba.
Tsakanin kungiyoyin kwallon kafan guda biyu kowacce bukatar nasara take yi a wasan na yau, shin ko waye zai yi nasara?
Lokaci ne dai zai nuna wanda zaiyi nasara ayau din.
Turawa Abokai
[…] Muƙalar Da Ta GabataKo Waza Awanke Tsakanin Arsenal da Manchester City? […]