Mutane Biliyan Ɗaya Ne Su Ka Nemi Aure Na – Aisha Tsamiya

5284

Fitacciyar jarumar wasan Kanywood Aisha Aliyu Tsamiya ta ce kimanin mutane biliyan ɗaya ne su ka so ta da aure amma har yanzu bata yi ba.

Aisha Tsamiya ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke tattaunawa da gidan rediyon Dala da ke Kano.

Jaruma Aisha Tsamiya tana daga cikin jarumai mata waɗanda ba su taɓa aure. Ta ƙara da cewa da zarar ta yi auren ta daina harkar film domin ba’a haɗa aure da film.

Sai dai a ƴan watannin an daina ganin fuskar jarumar a shirin fina-finan na Kanywood.
Madogara Dala FM, Kano

Turawa Abokai

7 Sako

  1. Aisha wai dole ne Sai kinyi karya ? Kodai bakije makaranta bane? Inajin bakisan me ake nufi da billiyan ba.
    Kin diba da fadi dan wani ko da Naira billiyan aka bashi ya aureki bazai aurekiba.

  2. Baya ga sanyi akwai yiwuwar mutanen boye sun rabe ki. Anya kin sa biliyan kwa?
    Tun mu na yara abin da muka sani tsamiya ta aljannu ce.

  3. Kaddara duk mutanen Nigeria mata da maza, yara da manya, marasa lafiya da masu tabin hankali sukeso su aureki, to ai ko mutanen najeriya gaba daya basukai 200 million ba. Ina kika samo ragowar 800million. Arage karya

  4. Uhmm to ai daman kinyi kinhuta ai kosokike sai kin tsufa kuma?

    Inma tarihine aikin kafa yakamata kuma ki barwa yan baya guri suma so taka irin tasu rawar.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan