Wani Ƙato Ya Angonce Da Ƴar Tsanar Roba

174

Yuri Tolochko ɗan ƙasar Kazakhstan zai auri Bebin Roba ta jima’i mai suna Margo.Ya yanke wannan shawarar ne bayan da ya biya aka yi wa Margo aiki.

Ya biya makudan kudade inda aka yi mata aiki don canza mata fuska. Kamar yadda Tolochko yace, ya hadu da Margo a mashaya ne.

Ya sanar da hakan ne a wani shirin gidan talabijin da aka gayyacesu don tattaunawa a kan dangantakarshi da Margo.

Tolochko ya ce: “Lokacin da na nunata a duniya, na fuskanci kalubale kuma kowa ya san fuskarta,a don haka ne na biya aka yi mata aikin canza kamanni ta sauya da yawa.

Rahotanni sun nuna cewa, dan wasan kwaikwayon na yi wa Babin Robar hidima tamkar mai rai don kuwa har aiki ya samar mata a wata mashaya.

Tolochko ya ce: “Ba ta iya tafiya ba, tana bukatar taimako. Margo bata iya girki ba amma tana son irin abinci yankin Georgia. Ta fi son Khinkali fiye da komai.” Kamar yadda yace, ya hadu da Margo ne a wata mashaya yayin da wani matashi ya kai mata hari. Shi kuwa ya bata kariya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan