Kar Wanda Ya Ƙara Biyan Haraji Ga Ma’aikatanmu A Hannu – Sani Dembo

109

Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano ta bukaci masu biyan haraji a jihar Kano da kar su ke bawa ma’aikatan hukumar kudi a matsayin hanya ta biyan haraji.

Shugaban hukumar Sani Abdulkadir Dembo ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na gidan Freedom Radio da ke Kano

Sani Dembo ya kara da cewa hukumar ta fito da tsare tsaren da mai biyan haraji zai bi ta banki kuma a ba shi rasiti wanda zai zame masa hujja.

Yace daga inganta hukumar zuwa yau hukumar tattara kudaden shigar ta jihar Kano na samun Naira biliyan biyu zuwa sama duk shekara.

Sani Dembo yace a baya kafin inganta hukumar gwamnatin Kano na samun Naira miliyan dari uku zuwa sama ne kacal a matsayin kudaden shiga.

Rahoton Freedom Radio Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan