Mun Rage Yawan Ƴan Adaidaita Sahu Daga Dubu Ɗari Biyu Zuwa Dubu Ɗari – KAROTA

90

Gwamnatin jihar Kano tace daga yanzu ta rage yawan adadin Baburan adaidaita sahu da zasu gudanar da sana’arsu a jihar Kano daga dubu dari biyu zuwa dubu dari.

Shugaban hukumar Karota ta jihar Kano Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da sabuwar koriyar lambar masu Adaidaita su a yau.

Baffa Babba Dan’agundi ya kara da cewa daga rana irin ta yau duk direban Adaidaita sahun daya sanya duk wani nau’in hoto a jikin babur dinsa ya zama wajibi ya biya hukumar Karota kudin talla.

Shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ya kuma shida cewa daga ranar irinta yau Karota ta soke duk wata alakar ta da kungiyar direbobin Adaidaita sahu ta TOAKAN sakamakon yunkurin tayar da hatsaniya kuma baza su dawo cigaba da alaka da kungiyar Tokan ba harsai jami’an tsaro na ‘Yansanda sun kammala gudanar da bIncike akan rahotan da suka mika musu.

A ƙarshe Baffa Babba Dan’agundi na cewa duk direban Adaidaita sahun da bai yi sabuwar rigistar ba har aka rufe yi a karshen wannan watan da muke ciki, Karota zata kara masa kudin tara matukar gwamnati taga damar sake bada dama ayi rigistar karo na biyu.

Rahoton Freedom Radio Kano

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan